Sunday, 8 April 2018

Shugaba Buhari zai tafi kasar Ingila Gobe

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya koma Abuja daga mahaifarshi Daura inda yaje gaisuwar marigayi sanata Mustafa Bukar wanda ya rasu makon daya gabata, bayan dawowa shugaban zai tafi Kasar Ingila Gobe, Litinin inda zai gana da Fraiministar kasar, theresa May.


A sanarwar da me magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya fitar tace shugaba Buharin zai gana da wasu sauran mutane a kasar kamin taron da zai halarta na kasashe rainon kasar Ingila.

Muna fatan Allah ya kaishi lafiya ya dawo dashi lafiya.

No comments:

Post a Comment