Wednesday, 4 April 2018

'Shugaba Buhari zaikai ziyarar sirri kasar Ingila'

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Ingila ranar Litinin me zuwa idan Allah ya kaimu kamar yanda wata majiya daga fadar shugaban kasar ta bayyana, saidai babu tabbacin abinda zaikai shugaba Buharin kasar ta Ingila.


Kamar yanda Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ta tuntubi me magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu akan wannan batu amma yaki yace komai akai. Shugaba Buharin dai zaije kasar ta ingilane kamin wani taron kasashe renon kasar Ingila da za'ayi a mako me zuwa.

No comments:

Post a Comment