Tuesday, 3 April 2018

Tsohuwar matar Mandela, Winnie, ta rasu

Tsohuwar matar marigayi Nelson Mandel, Winnie, ta rasu tana da shekara 81 a duniya. Mai magana da yawun iyalanta Victor Dlamini ya ce: "Ta rasu ne bayan ta yi fama fa doguwar jinya a safiyar ranar Litinin."An haifi marigayiyar ne a shekarar 1936 a lardin Eastern Cape wanda a da ake kira Transkei.
Ta fara haduwa ne da Mandela a shekarun 1950 kuma sun kwashe shekara 38 a matsayin ma'aurata - kodayake kimanin shekara 30 ba sa tare da juna saboda Mandela yana gidan yari.

Duk da cewa aurensu ya mutu a shekarar 1996, Winnie ta ci gaba da amfani da sunan Mandela da kuma hulda da shi.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment