Saturday, 14 April 2018

Tunatarwa akan amfani da yanar gizo>>Tijjani Asase

Tauraron fina-finan Hausa, Tijjani Asase yayi kira ga ga mutane da su lura da irin abubuwan da suke rubutawa a dandalinsu na sada zumunta na yanar gizo, inda yace idan ana so a san ko wane irin mutum ne kai da an duba dandalinka na sada zumunta za'a iya fahimtar hakan.


Gadai abinda ya rubuta kamar haka:

"Atunanina tarbiya agida akesamunta, shiyasa bana daga hankalina idan naga mutane suna rubuce rubuce, awannan dan dalin, atunanina idan karubuta wani abu awannan dandalin,ko Babanka ko kaninsa ko dan uwansa ko surikanka ko abokan babanka, wani zaigani acikinsu koda sharri karubuta ko alkairi. kuma atunanina ko awre kaje nema idan ana san asan waye kai daza shiga dan dalinka,na Sada zumuta, da ya isa mutane shedar sanin wayekai. zakaga mutun ya sami sa'an kakansa ko babansa yana ragar gazar sa wai sabida ya shiga siyasa ko kaga yaro ya dakko hotan wani babban malami ya hada da Mace kuma yayi rubutu kalma marradadi, sabida kawai ba akidarsu daya ba,kaga ansa wa babban mutun fiskar Kare ko buri. kamanta idan yagani zai ce Allah ya isa, kuma katuna Allah yace baya yafe hakin wani, yazakai da wannan hakkin dan uwa muji storan Allah."

No comments:

Post a Comment