Sunday, 1 April 2018

'Yan kasar Egypt fiye da miliyan daya sun zabi Muhammad Salah a matsayin shugaban kasa

A zaben shugaban kasar da akayi a kasar Misra/Egypt an samu fiye da masu zabe miliyan daya sun bayyana dan wasan kasar, Muhammad Salah a matsayin wada suke so ya zama shugaban kasa, masu zaben dai sun soke sunayen 'yan takarar dake jikin kuri'ar suka rika rubuta sunan Muhammad Salah abinda yasa aka mayar da kuri'un nasu wanda basu cikin lissafi.


Yawan kuri'un da Salah din ya samu dai da ace suna cikin lissafi to shine yazo na biyu bayan shugaban kasar, Abdel Fatah Al-sisi da ya lashe zaben. Kamar yanda kafofin labaraida dama suka bayyana.

Muhammad Salah dai na kara haskakawa a kungiyarshi ta Liverpool inda yaci kwallaye talatin da shida a wasanni arba'in da daya da ya buga, haka kuma shine yaci kwallon da ta kai kasarshi ga gasar cin kofin kwallon Duniya, a yanzu dai bayan Cristiano Ronaldo da Lionel Mesii, sunan Salah ake kira a fagen haskakawa a Duniyar kwallo.

No comments:

Post a Comment