Monday, 16 April 2018

Yanda aka ga kwalaben kodin a jakunkunan matan da suka taru a wani gidan suna

Wani bawan Allah ya bayar da labarin yanda aka samu kwalaben kwayar kodin a jakunkunan yawancin matan aure da suka taru a wani gidan suna a Kano, yace, kudi sun bace a wani gidan suna dake garin Kano, sai aka bukaci duk matan dake gidan su bayar da jakunkunansu dan ayi caje.


Abin mamaki kusan dukkan jakunkunan matan da aka duba sai da aka ga kwalbar kodin kuma matan aure sunfi yawa a ciki.

Allah ya shiryar damu.

No comments:

Post a Comment