Pages

Thursday 19 April 2018

'Yanzu lokacin zabene ya kamata ya iya bakinsa'>>Ra'ayin Dr Aminu Gamawa akan maganar shugaba Buhari ga matasa

Lauya‪ kuma malami, Dr. Aminu Gamawa ya bayyana ra'ayinshi akan maganar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi dangane da matasan Najeriya kamar haka:

Mutumin namu wani lokaci da Hausa yake tunani shi yasa idan ya furta wasu kalaman da turanci sai kaga sun bada ma’ana wanda ba lalle ne ta gamsar ba. Yanzu lokacin zabe ne. Ya kamata ya iya bakinsa. Ya guji kalamai da za’a iya sauya musu ma’ana ko kuma masu kawo cece-kuce. ‬



‪“Yawancin matasanmu basu yi karatu ba, kuma sun kashe jiki suna jiran Gwamnati ta yi musu komai.” ‬

‪Wannan shine abunda ya fada. Da Hausa yayi ma’ana kuma gaskiyane. Amma idan ka maida shi turanci, musamman yadda ya fada, sai kaga kamar akwai raini ko rashin tausayi.‬

Babu wanda suka taimaki shugaba Buhari wajen cin zabe kamar matasa, wanda suka yi karatu da wanda basu yi ba. Idan ba’a dora Amarya a kan doki ba, to kar a dora mata kaya. Wanda suka yi karatun ma ba kowane yake samun aiki ba sai masu gata.

No comments:

Post a Comment