Monday, 16 April 2018

'Yayinda hankalin 'yan siyasar Najeriya ya karkata akan zabe, nikuwa na mayar da hankaline kan samar da tsaro da habaka tattalin arziki'>>Shugaba Buhari

A ganawar da yayi firaiministar Ingila, Theresa May, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a lokacin da zabe ke matsowa, hankalin 'yan siyasa ya raja'a akan zabe shi kuwa yafi meda hankali akan tsaro da cigaban tattalin arzikin kasa.Shugaba Buhari ya kuma bayyana irin yanda gwamnatinshi ta baiwa harkar noma muhimmanci inda yace a da matasa da dama sun bar kauyuka sun dawo birni dan neman kudin mai, amma yanzu saboda irin tsari mekyau da suka fito dashi na harkar noma da dama, ciki hadda kwararrun ma'aikata na komawa harkar noma.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa janyewar tafkin Chadi ba karamin illa yayi ga kasashen dake zagaye da tafkin ba inda yace da za'a dawo da ruwan tafkin to da miliyoyin matasa sun samu aikinyi.


Ya kuma kara da cewa hakan zai rage yawan kwararar matasa zuwa kasashen turai dan neman ayyukan yi, shugaba Buhari ya bayar da misali da 'yan Najeriya da dama da aka dawo dasu daga kasar Libiya dake kokarin haurawa kasashen turai inda yace yawancinsu ' yan kasa da shekaru talatinne.

Shugaba Buhari ya kuma yabawa kamfanonin kasar Ingila da suke gudanar da kasuwancinsu a Najeriya inda yace duk da halin da Najeriya ta samu kanta basu taba barin kasarba, ya bayar da misali da kamfanoni irin su Cadbury da Unilever inda yace yana fatan kamfanonin kasar ta Ingila zasu kara yawan saka jari a Najeriya.

Ya kuma Godewa kasar ta Ingila bisa irin taimakon ta take baiwa Najeriya ta fannoni da dama da suka hada da tsaro da tattlin arziki, ya kuma kara da cewa gwamnatinshi na baiwa fannin ilimi muhimmanci dan samar da cigaba a tsakanon al'umma.

Da take jawabi a ganawar tasu, Theresa May ta bayyana cewa, kasarta zata cigaba da baiwa Najeriya irin tallafin da take bata na harkar cigaba sannan kuma ta yabawa gwamnatin shugaba Buhari akan habbaka harkar tattalin arziki da takeyi.

Ta kuma yi kira da a baiwa bangaren ilimi muhimmanci inda tace ta hakanne yara masu tasowa zasu kaucewa cin zarafi, bautarwa da kuma sanin yanda zasu gudanar da rayuwarsu cikin tsari, kamar yanda yazo a sanarwar da me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar.

No comments:

Post a Comment