Thursday, 26 April 2018

Za a mayar da dajin Sambisa wurin yawon bude ido

Babban Hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar janar Tukur Buratai ya bayyana aniyar mayar da dajin yankin Sambisa, mabuyar Boko Haram zuwa wurin yawon bude ido.


Ya ce sojoji za su yi aiki tare da hukumar kula da wuraren yawon bude ido ta kasa domin ta taimaka wajan farfado da kimar dajin, domin masu yawon bude ido daga kasashen ketare su samu damar ganin namun daji.

Mayakan Boko Haram sun yi amfani da wasu sassa na dajin a matsayin mabuyarsu yayin da suka rika tada kayar baya a yankin arewa maso gabashin kasar.

Sai dai rundunar sojin kasar ta yi ikirarin cewa ta kore mayakan daga cikin dajin.
Wani mai ba Shugaba Muhammadu Buhari shawara ne kan harkokin watsa labarai ya wallafa kalaman hafsan sojin kasan a shafinsa na Twiiter.

"Rundunar sojin Najeriya za ta hada gwiwa da hukumar kula da wuraren yawo bude ido ta kasa da gwamnatin jihar Borno domin maida dajin Sambisa a matsayin wurin yawon shakatawa da nufin jan hankalin masu yawon bude ido zuwa kasar," in ji Janar Buratai.

A lokacin Turawa ma su mulkin mallaka dajin Sambisa wurin ne na masu yawon shakatawa amma daga baya dajin ya koma wurin da Boko Haram suke samun mafaka bayan sun kai hari.

Iyayen dalibai mata na sakandaren gwamanti da ke garin Chibok, su 230 da aka sace a shekarar 2014 sun yi barazanar shiga cikin dajin a lokacin da alamarin ya faru.

Dajin ya ratsa ta jihojin Borno da Yobe da Gombe da Bauchi da Jigawa da kuma Kano.

A shekarar 1991 ne gwamnatin jihar Borno ta sa wurin ya koma karkashin hukumar kula da wuraren yawon bude na tafkin Chadi `

A wancan lokacin akwai namun daji irinsu Zaki da Giwa da Kura da tsuntsaye da kuma gidajen laka musu jinka da aka gina domin masu yawo bude ido.

Sai dai rashin kula ya sa dabbobin da ke dajin mutuwa kuma gidajen lakan da hanyoyin da ake bi suka lalace, kuma babu ruwan sha da wutar lantarki.
bbchausa.


No comments:

Post a Comment