Tuesday, 3 April 2018

ZABEN 2019: Kanu Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa

Fitaccen dan wasan kwallon kafa Kanu Nwankwo, ya bayyana cewar zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019 dake tafe. Kanu ya sha alwashin cewar, zai kawo karshen mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019. Kanu ya kara da cewar shekaru 18 da suka shude babu abunda gwamnatoti suka yi banda jefa 'yan Nijeriya cikin halin kunci da rashin tsaro. 


Kanu ya yi wannan kalami ne a lokacin da yake hira da kamfanin jaridar wasanni ta Goal.com. Shafin jaridar Daily post, ta nakalto Kanu na cewar "Nasarar da George Weah yasamu a zaben kasar Liberia, yar manuniya ce ga tabbatuwar mafarki na idan har yan Najeriya suka mara min baya.

Sai dai Kanu bai bayyana jam'iyar da zai tsaya takara cikin ta ba.ZABEN 2019: Fitaccen dan wasan kwallon kafa Kanu Nwankwo, ya bayyana cewar zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019 dake tafe.

Kanu yasha alwashin cewar, zai kawo Karshen mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019. Kanu ya kara da cewar shekaru 18 da suka shude babu abunda gwamnatoti sukayi banda jefa yan Najeriya cikin halin kunci da rashin tsaro. 

Kanu yayi wannan kalami ne a lokacin da yake hira da kamfanin jaridar wasanni ta Goal.com. Shafin jaridar Daily post, ta nakalto Kanu na cewar "Nasarar da George Weah yasamu a zaben kasar Liberia, yar manuniya ce ga tabbatuwar mafarki na idan har yan Najeriya suka mara min baya.

Sai dai Kanu bai bayyana jam'iyar da zai tsaya takara cikin ta ba.
rariya.

No comments:

Post a Comment