Tuesday, 3 April 2018

Zahara Buhari ta yiwa kawunta fatan rayuwar aure me Albarka

Zahara Buhari ta yiwa kawunta, kanin Mahaifiyarta, Hamza Halilu da matarshi Hadiza fatan Alheri a aurensu da suka yi kwanannan, Zahara ta bayyanashi a matsayin mutumin kirki wanda ke da halayya ta gari.


Tace koda yaushe suna tare dashi a lokacin da sukayi makaranta tare kuma yakan basu shawara akan harkokin rayuwa daban-daban, a karshe ta musu fatan yin rayuwar aure me tsafta.

No comments:

Post a Comment