Wednesday, 11 April 2018

'Zamu saka Buhari cikin addu'a kan tsayawarshi takara>>Inji Wani limamin coki a kasar Ingila

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan tare da limamin cocin Aglican dake kasar Ingila, Archbishop Justin Welby daya ziyarceshi a masaukinshi dake kasar ta Ingila, Welby ya shaidawa shugaba Buhari cewa yaga labarin bayyana tsayawa takarar shugaban Najeriya a zaben 2019 da yayi inda ya tabbatar mai da cewa zasu sakashi cikin addu'a.


Welby ya bayyana cewa su 'yan ba ruwansu da kowane, watau basu da wanda suke goyon baya amma duk da haka zasu saka shugaba Buharin cikin addu'a.

No comments:

Post a Comment