Thursday, 17 May 2018

Abin tausai: Kotu ta wanke mutumin da aka daure shekaru 27 bisa kuskure

Wani mutum me suna John Bunn kenan a wannan hoton dan Brooklyn dake kasar Amurka da aka daureshi tsawon shekaru goma sha bakwai bisa kuskuren kisan da be aikataba, tun yana dan ahekaru sha hudu aka kamashi tare da wani shima dan shekaru sha shida me suna Hargrave duk bisa kuskure.


Bayan shafe shekaru sha bakwai a gidan yari, a shekarar 2009 an yiwa John sakin talala inda a haka ya ci gaba da fafutukar ganin ya wanke sunanshi, tun yana daure a kurkuku yasha bayyana cewa shi be aikata laifin da ake zarginshi dashi ba.

Wasu 'yansanda biyune dake bakin aiki aka fito dasu daga motarsu aka harbesu da bindiga aka kuma sace motar tasu, daya daga cikin 'yansandan ya mutu, daya kuma ya tsira bayan yayi jiyya, shine ya bayar da sheda akan wadanda suka musu wancan danyen aiki. Wani dansanda da ya gudanar da bincike akan lamarinne me suna scarcella ya saka hotunan wadannan matasa guda biyu cikin fayil din Case din.
John lokacin yana karamin yaro, tun yana da shekaru 14 aka zargeshi da laifin kisan da be aikataba.

Binciken da akayi an gane cewa Scarcella ya aikata irin wadannan halayya ta aikata ba daidai ba ga mutane da dama lokacin yana aiki akan kyasa-kyasai na kisa, dan haka ake bin dukkan aikin da yayi bincike akanshi dan gano gaskiyar abinda ya faru.

A lamarin John da abokinshi an gano cewa a rana daya aka musu shari'a aka saurari shaidu aka kuma dauresu, wanda hakan kawai ya isa ya bayar da dalilin cewa ba'ayi adalci a shari'ar tasu ba, haka kuma karin bin ciken da akayi ya bayyana hotunan zanen hannun da aka samu a gurin laifin beyi daidai dana yaran ba.

Yanzu dai kotu ta wankesu daga wannan laifi bayan shekaru ashirin da bakwai suna fama, John yanzu wanda yake da shekaru arba'in da ya, ya fashe da kuka a kotun bayan da aka bayyana cewa an wankeshi daga laifi.

Ya gayawa kotun cewa  nagode , shekaru ashirin da bakwai kenan ina ta faman tseratar da rayuwata, kun kamani ban aikata laifin ba shi kuwa wanda ya aikata yana can yana yawonshi abinshi a kan titi.


Shekaru ashirin da bakwai kenan, ya karasa gaban alkalin inda ya kama hannunta ya hada kai da teburin gaban ta yana kwalla, haka ma mahaifiyarshi da ta halarci sauraron karar itama ta fashe da kuka.

Shima Hargrave a wata shari'a ta daban da aka gudanar an wankeshi daga laifin kisan inda shima da mahaifiyarshi da budurwarshi suka yi ta kuka a kotun, shima dai yanzu shekarunshi arba'in da hudu da haihuwa.

Lokacin da yake hira da manema labarai a wajan kotun ya bayyana cewa, wani irin duka da wani jami'in tsaro ya taba mishi lokacin yana daure saida ya hango mutuwa, duk akan laifin da be aikataba. Ama yace ya godewa Allah zai ci gaba da rayuwarshi yanzu.
The Sun.

No comments:

Post a Comment