Thursday, 17 May 2018

An daure dan tsohon shugaban kasa saboda satar wayar hannu

Matar tsohon shugaban kasar Zambia, Vera Chiluba tare da danta Fredrick Chiluba karami a shekarar 2014 lokacin da ya kammala makarantar horar da sojin sama na kasar
Wata kotu a kasar Zambia ta yankewa dan tsohon shugaban kasar hukuncin daurin watanni takwas a gidan yari da horo me tsanani saboda samunshi da laifin satar wayar hannu da akayi, 


Dan shugaban kasar me suna Fredrick Chiluba ya saci wayar kirar Samsung da kudin ta ya kai dalar Amurka dari takwas da arba'in da uku a shekarar data gabata daga hannun wata mata, rahotanni sun bayyana cewa ya bayar da wayar inda aka musanya mai da kwaya.

Alkalin kotun dake babban birnin kasar Lusaka, me suna Chabala ta ce hujjojin da aka gabatar mata sun tabbatar da cewa dan shugaban kasar yayi satar dan haka ta yankemai hukunci.

Mahaifin shidai me suna Chibula babba ya mulki kasar Zambia daga shekarar 1991 zuwa 2001, bayan saukarshi daga mulki an zargeshi da laifukan rashawa da cin hanci.

No comments:

Post a Comment