Wednesday, 16 May 2018

An fara azumin Ramadan a Nijar

Al'ummar Musulmi a Jamhuriyar Nijar sun fara azumin watan Ramadan ranar Laraba bayan ganin jinjirin watan a wadansu yankuna na kasar a ranar Talata. Firai Ministan kasar Briji Raffini ne ya sanar da ganin jinjirin watan azumin a wadansu yankuna na kasar.


Sai dai ba a fara azumin ba a makwabciyar kasar ba, wato Najeriya, saboda a ranar Laraba ne za a fara neman jinjirin watan bayan Majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta bukaci hakan a farkon makon nan.

Ita ma kasar Saudiyya za ta fara azumin ne a ranar Alhamis bayan hukumomin kasar sun sanar da cewa ba a ga watan ba a fadin kasar a ranar Talata, wadda ta kasance 29 ga watan Sha'aban.

Hakazalika sauran kasashen Musulmin ciki har da Indonisiya za a fara azumin ne a ranar Alhamis.

Batun fara azumi da ajiye shi yana yawan jawo ce-ce-ku-ce a kasashen duniya musamman a Najeriya.

Ramadan dai wata ne da Musulmi suke kauracewa ci da sha da kuma jima'i daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana, inda suke matsa kaimi wurin ibada da addu'o'i.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment