Tuesday, 15 May 2018

An fidda sunayen masu buga wa Najeriya gasar cin kofin duniya

An fitar da sunayen 'yan wasa 30 cikin wadanda ake sa ran za su wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya da za a yi a watan Yuni.


Cikin 'yan wasa dai akwai manyan 'yan wasa irin su Victor Moses da ke taka leda a Chelsea da Ahmed Musa da ke CSKA Moscow da kuma Shehu Abdullahi da ke Busarpor a Turkiyya.

Ana sa ran cewar cikin wadannan 'yan wasan ne dai za a dauki 'yan wasa 22 da za su buga gasar cin kofin duniya a Rasha.

Ga jerin sunayen mutanen:

Masu tsaron gida:

Ikechukwu Ezenwa da Daniel Akpeyi da Francis Uzoho da kuma Dele Ajiboye

Masu tsaron baya:
William Ekong da Leon Balogun da Ololuwa Aina da Kenneth Emeruo da Bryan Idowu da Chidozie Awaziem da Abdullahi Shehu da Elderson Echiejile da Tronne Ebuehi da kuma Stephen Ezeh.

'Yan wasan tsakiya:
Mikel Obi da Ogenyi Onazi da John Ogu da Wilfred Ndidi da Uche Agbo da Oghenekaro Etebo da Joel Obi da kuma Mikel Agu.

'Yan wasan gaba:
Odion Ighalo da Ahmed Musa da Victor Moses da Alex Iwobi da Kelechi Iheanacho da Moses Simon da Junior Lokosa da kuma Simeone Nnwakwo.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment