Tuesday, 15 May 2018

An gurfanar da Sheikh Zakzaky a gaban kotu a Kaduna


Shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi ta 'yan Shi'a (IMN) Sheikh Ibrahim el-Zakzaky da matarsa sun bayyana a gaban wata babbar kotu da ke jihar Kaduna ranar Talata. Gwamnatin jihar Kaduna na tuhumarsa da kisan wani soja lokacin wani rikici da magoya bayansa suka yi da sojoji a garin Zariya a shekarar 2015.
Sai dai sauran mutane biyu da ake zarginsu tare wadanda suka hada da Sheikh Yakoub Yahaya Katsina da Sheikh Sanusi Abdulkadair Koki ba su bayyana a gaban kotu ba.

Kotun ta karanta wa jagoran 'yan Shi'a tuhumar da ake yi masa, sai dai Sheikh Zakzaky ya musanta zargin.

Lauyan da ke kare Zakzaky Barista Maxwell Kenyon ya nemi kotun ta ba da belinsa, sai dai alkalin kotun ya yi watsi da bukatar.

Mai Shari'a Kurada ya nemi lauyan a kan ya gabatar da bukatar neman belin a rubuce.

Lauyan masu shigar da kara Daris Bayero ya bukaci kotun ta amince wa hukumar tsaro ta DSS ta ci gaba da tsare jagoran a hannunta.

Kotun ta amince da hakan, san nan daga bisa an mayar da Sheikh Zakzaky Abuja.

Daga nan kotun ta dage zamanta zuwa ranar 21 ga watan Yuni.


Sai dai a cikin sanarwar da kungiyar 'yan Shi'a ta fitar ta ce ta yi watsi da matakin da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka.

Sanarwar da ke dauke da sa hannun daya daga cikin shugabannin kungiyar Sheikh Abdulhamid Bello ya ce sun dauki matakin a matsayin takalar fadan magoya bayan malamin.

Ya kuma ce "alhaki na kan gwamnatin tarayya idan wani abu ya faru da Zakzaky."

A karshe Sheikh Abdullahi Bello ya ce mambobin kungiyarsu za su ci gaba da zanga-zangar neman a sako musu jagoransu.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment