Monday, 21 May 2018

'Yansanda sun kama matashi saboda ya musulunta

Jami'an 'yansanda sun kama wani matashi dan shekaru 21 bayan da 'yan uwanshi suka kai kara gurin 'yansandan inda suka zargi cewa tirsasa mai shiga musuluncin akayi,  saidai matashin ya shaidawa 'yansandan cewa babu wanda ya tursasashi, da kanshi ya shiga addinin musulunci.


Matashin dan yankin Baraula Jafrabad dake kasar Indiya, mabiyin addinin Hindune a baya, kamin ya fara aiki da wani shagon kafintoci inda anan ne ya musulunta, ya canja suna daga Ved Prakash zuwa Aadil,  kuma har yaga wata budurwar musulma zai aura, anan ne fa mahaifanshi sukace basu yardaba, inda suka hada kai da wata kungiyar masu tsatsaura'ayin addinin Hindu suka kai kara gurin 'yansanda, sun bayyana cewa aun so suga dansu amma jama'ar dake ahagon suka hanasu suka kuma musu barazanar kada su sake su gayawa hukima.

Watanninshi takwas kenan da musulunta, sai jiya Lahadi, 'yansanda suka kamashi saboda karar da danginshi suka kai, 'yan uwan nashi sun bayyanawa hukuma cewa yarinyar da ya gani yana so ce tasa ya musulunta, saboda dan uwanta yace mai sai ya musulunta zai aura mishi ita, amma Aadil ya musanta wannan magana inda yace bisa aradin kanshine ya musulunta kuka baya danasanin yin hakan.

Yanzu dai an kama dan uwan budurwar Aadil, me suna Wasim wanda ake zargi da tirsasa mishi musulunta haka kuma an kama wani shima wanda ake zargi yana da hannu akan lamarin.
Times of india.

1 comment:

  1. Kai may Allah free our muslims for those dont have freedom!!!

    ReplyDelete