Thursday, 17 May 2018

An tura tsohon gwamnan jihar Filato gidan wakafi

Tsohon gwamnan jihar Filato Jonah Jang ya bayyana a gaban wata babbar kotu da ke jihar Flato bi sa zargin almundahana da ake yi masa. Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzkin kasa ta'anati (EFCC) ce ta gurfanar da shi a gaban kotu kan tuhumar almundahana da kudi fiye da naira biliyan shida lokacin da yake rike da mukamin gwamna.Ana zargin Jonah Jang wanda yanzu sanata ne a majalisar dattawan Najeriya da yin sama da fadi da naira biliyan 2 na talafin da babban bankin Najeriya ya bada domin bunkasa kananan masana'antu a jihar, watani biyu kafin wa'adinsa kan mulki ya zo karshe a shekarar 2015.

Hukumar EFCC na kuma zarginsa da wawure kudi fiye da naira biliyan hudu daga asusun gwamnati ta hanyar amfani da ofishin sakataren gwamnati na wancan lokaci Yusuf Gyang Pam wanda ake tuhumarsa tare.

Sai dai tsohon gwamnan da Mista Pam din sun musanta zargin da ake yi musu bayan da aka karanta tuhumar.

Lauyan hukumar EFCC, Rotimi Jacobs ya nemi kotu akan ta ba su damar ci gaba da tsare mutanen biyu har zuwa ranar da za ta saurari bukatar belin da aka shigar a gabanta.

Amma lauyan da ke kare Jonah Jang, Robert Clarke ya nemi kotun a kan ta ba da belinsa saboda tsohon gwamnan ne a lokacin mulki soja da kuma mulkin dimokradiya kuma yanzu dan majalisar dattawa ne.

A karshe alkalin kotun Mai Shari'a Daniel Longji ya yi watsi da bukatar Jonah Jang kuma ya ba da umarnin ci gaba da tsare shi a gidan wakafi har zuwa lokacin da zai sake saurarar bukatar neman belin.

A ranar 24 ga watan Mayu ne kotu za ta saurari bukatar tasa.
bbchausa

No comments:

Post a Comment