Wednesday, 16 May 2018

Anga jaririn watan Ramadana a wasu jihohin Najeriya

Rahotanni daga sassan Najeriya daban-daban sun bayyana cewa anga jaririn watan Ramadana, Jihohin Adamawa, Kano, Gombe da sauransu na daga cikin jihohin da aka ga watan.


Haka ma kasar Saudiyya ta bayyana ganin jaririn watan a yau wanda hakan ke tabbatar da cewa gobe za'a tashi da Azumi a kasar.

Zuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da aka samu daga Najeriya akan ganin watan.

No comments:

Post a Comment