Tuesday, 15 May 2018

Anyi musayar yawu tsakanin Classiq da Morell

Wani rashin fahimta yaso ya shiga tsakanin taurarin mawakan gambara na Arewa, watau Classiq da Morell, inda har ta kai ga Classiq din ya rubutawa Morell budaddiyar wasika da ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta, maganar dai akan wata wakace da sukayi tare me suna 'Ba Wani Bughatti' wadda Morell din ya saki ba tare da sanin Classiq ba.Classiq ya bayyana cewa yaji dadin kasancewa a cikin wakar da akayi amma abinda ya batamai rai shine yanda aka sauya salon wakar aka kuma sake ta ba tare da sanar dashi ba, ya kuma cewa idan dai ba anyi da wata manufa bace ta daban ya kamata ace yasan da wannan lamari.

A nashi bangaren, Morell ya bayar da amsar cewa wani abokin aikinshine yayi wannan canje-canje a wakar ya kuma sake ta saboda doki, ba tare da saninshi ba, ya kara da cewa bashi da niyyar sakin wakar yanzu dan yana ganin lokaci be yiba.

Amma a karshe yana baiwa Classiq din hakuri akan wannan lamari ba zai taba yin wani abu da zai bata musu sana'a ba, ya kuma kara da cewa, aikinsu yayi magoya bayansu sun nuna soyayya sosai.

No comments:

Post a Comment