Thursday, 17 May 2018

Arteta ya cancanci ya gaje ni>>Wenger

Arsene Wenger ya ce Mikel Arteta na da duk abubuwan da ake bukata domin ya gaje shi a matsayin kocin Arsenal. Tsohon kyaftin din kulob din Arteta na cikin wadanda ake sa ran za su maye gurbin Wenger, wanda ya bar kungiyar a karshen wannan kakar bayan shafe shekara 22.


Dan kasar Spaniya, mai shekara 36, ya buga wasa 150 a Arsenal kuma a yanzu yana daya daga cikin kociyoyin Manchester City.

"Jagora ne na gaske, yana sha'awar wasan, ya fahimci kulob din kuma ya san abin da ke da muhimmanci a kungiyar," a cewar Wenger.

Arteta, wanda bai taba jagorantar wata kungiya ba, ya karbi aiki a karkashin kocin City Pep Guardiola a 2016.

Wenger, mai shekara 68, ya shaida wa Bein Sports cewa: "Idan ka yi la'akari da lamarin baki daya za ka ga cewa yana da duk abin da ake bukata, amma ba na so na fadi hakan a bainar jama'a."

Arsenal ta kuma tuntubi wani tsohon dan wasan nasu Patrick Vieira, a wani yunkuri na neman wanda zai maye gurbin Wenger.

Kulub din na sa ran nada wanda zai gaji Bafaranshen kafin a fara gasar cin kofin duniya a ranar 14 ga watan gobe.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment