Thursday, 17 May 2018

Atletico ta lashe Europa League

Atletico Madrid
Kungiyar Atletico Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai na Europa a bana, bayan ta ci Marseille 3-0 a wasan da suka kara a Lyon.


Atletico Madrid
Wannan shi ne kofi na uku da Atletico ta lashe kofin, ita kuwa Marseille ba ta taba cin kofin ba.
A ranar 26 ga watan Mayu ne za a buga wasan karshe a babbar gasar Zakatun Turai tsakanin Liverpool da Real Madrid a birnin Kiev din Ukraine.
Wasu hotunan yadda 'yan wasan Atletico suka yi murna a Lyon.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment