Wednesday, 16 May 2018

Ba kai kadaine dan Najeriyar da baya son cin hanci ba>>Yakubu Dogara ya gayawa shugaba Buhari

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya bayyanawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa ba shi kadaine mutumin da baya son ta'amuli da rashawa da cin hanci ba a kasarnan, Dogara ya bayyana hakane a gurin taron bude ofishin hukumar EFCC da akayi jiya a Abuja.


Dogaran yayi jawabin cewa, anan muna tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari wanda Duniya ta amince cewa mutum ne na gari wanda baya lamuntar rashawa ko cin hanci a al-amuranshi.

Amma musani cewa ba shi kadai ne me irin wannan halayya a kasarnan ba, akwai tarin mutane da muke haduwa dasu a ayyukan mu na yau da kullun da basa ta'ammuli da rashawa kuma ya kamata mu fahimci hakan.

Dogara ya bayyana cewa domin karawa jami'an wannan hukuma ta EFCC kwarin gwiwa wajan yakar cin hanci da kuma kawar da hankalinsu wajan shiga a dama dasu a harkar cin hanci, ya kamata gwamnati ta inganta yanayin aikinsu, haka kuma ya yabawa gwamnatin akan ginin sabon ofishin hukumar.
Dailytrust.

No comments:

Post a Comment