Tuesday, 22 May 2018

Bani da ra'ayin tsayawa takarar Gwamna: Ni ba dan siyasa bane>>Magu

Shugaban riko na hukumar hana yiwa arzikin kasa ta'annati, EFCC, watau Ibrahim Magu ya karyata wani labari dake cewa wai yana son tsayawa takarar gwamnan jihar Borno saboda ya samu kariya daga tuhumar da za'a iya mishi bisa wasu zarge-zargen aikata ba daidai ba da yayi.


Labarin dai da wata kafar watsa labarai ta yanar gizo ta wallafa tace shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da tsohon gwamnan jihar Bornon, Madu Shareef dan samarwa Magu din hanyar da zai zama gwamnan Borno cikin sauki.

Saidai a sanarwar da ya fitar ta nannun me magana da yawun hukumar EFCC, Magu ya karyata wannan labari wanda yace bashi da tushe ballantana makama, yace shi ba dan siyasa bane, abinda ke gabanshi shine ganin ya aiwatar da aikin da gwamnatin tarayya ta bashine bisa ka'ida amma bashi da ra'ayin tsayawa takara.

Sanarwar tace danganta Magu da siyasa cin fuskarshine, domin shi mutumne me kokari wajan gundanar da aikin dake gabanshi, kuma Duniya ta shaida haka idan akayi la'akari da mukamin da aka bashi kwanannan na shugaban hukumomin yaki da cin hanci na kasashen nahiyar Afrika.

A karshe sanarwar tace, Magu ya gayawa lauyanshi ya dauki matakin daya dace akan kafar da ta buga wannan labari a kanshi. Vanguard.

No comments:

Post a Comment