Sunday, 27 May 2018

Bigewar da Ramos yawa Salah: Saikace ana kokawa?: Abin ya razana 'yan wasan Liiverpool>>Klopp

Da yake magana da manema labarai bayan kammala wasan jiya, Kocin Liverpool, Klopp ya bayyana cewa ciwon da Muhammad Salah yaji ya kada 'yan wasanshi sosai sannan kuma Madrid sunyi amfani da hakan wajan kara kaimin samun nasarar da sukayi.


Klopp ya bayyanawa Skysport cewa duk da yake yanzu idan yayi magana za'ace korafine irin na wanda yayi rashin nasara amma tabbas ciwon da Salah yaji ya razana 'yan wasanshi kuma hakan ya bayyana a fili.
Ya kara da cewa irin abinda Ramos yawa Salah kwata-kwata be dace ba, sai kace ana kokawa?, fadawa yayi akan hannunshi, raunine sosai, yanzu haka yana asibiti za'a dauki hoton hannun, kodai kashin kafadarshi ko kuma na kwalarshi ne ya samu matsala.
Klopp ya kara da cewa Madrid sunyi amfani da wannan damar wajan kara kwazon ganin sun yi nasara, ya yabawa Bale saboda irin hazakar da ya nuna a wasan inda yace kwallayen da akaci basu yi tsammaninsu ba.

Amma ya kara da cewa dama wasan karshe haka yake: mutum yana bukatar sa'a amma su basu sametaba kuma zasu cigaba da jimami.

No comments:

Post a Comment