Wednesday, 16 May 2018

Fabregas ya auri mace me 'ya'ya biyar

Tauraron dan kwallon kafar Chelsea, Cesc Fabregas ya auri budurwarshi da suka dadde suna soyayya tare me suna Danieĺla Semaan wadda kuma suka haifi 'ya'ya uku tare, dan kwallon ya saka hotunan shagalin auren nasu a dandalinshi na sada zumunta da muhawara.


Kamin su fara soyayya Semaan na da 'ya'ya biyu wanda ta samu daga tsohon masoyinta. Tun shekarar 2011 suke soyayya, sai yanzu ne suka yi aure. Ga wasu karin hotunan shagalin auren nasu.

Fabregas wanda tsohon dan kwallon Arsenal da Barcelona ne ya nuna farin ciki da wannan aure nashi sosai haka otama masoyiyar tashi.


No comments:

Post a Comment