Friday, 18 May 2018

Gianluigi Buffon: Zai buga wasansa na karshe a Juventus

Buffon
Golan Italiya Gianluigi Buffon ya sanar da cewa zai buga wasansa na karshe a Juventus a ranar Asabar bayan shafe shekaru 17 a kulub din.Kaftin din na Juventus mai shekara 40 zai karbi kofin gasar Seria A a karo na tara a karawar da za su yi da Hellas Verona a karshen mako.


Golan ya ce ya sauya tunani game da ritayarsa kwanaki 15 da suka gabata, saboda yadda ake tuntubarsa da wani aikin a ciki da wajen fili.
Buffon ya sanar da yin ritaya daga buga wa Italiya wasa bayan sun kasa samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha.
"Makon gobe, kwana biyu zuwa uku, zan yanke shawara," in ji Buffon.
Golan na Juventus na fuskantar barazanar dakatarwa daga hukumar kwallon Turai Uefa saboda kalaman da ya furta wa lafarin Ingila Michael Oliver bayan ya ba shi jan kati a karawarsu da Real Madrid a gasar Zakarun Turai.
Gianluigi Buffon
A lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, Buffon "ya nemi gafara."
Ya ce: "Idan muka sake haduwa da lafari, zan rungume shi mu gaisa da juna."
Buffon wanda Juventus ta karbo daga Parma a 2001, ya ce ba zai iya koma kama gola a wata kungiyar Italiya ba, inda ya ce yana son ya samu hutu na akalla wata shida.
Buffon ya jagoranci Juventus a matsayin kaftin ga nasarar lashe kofi bakwai na Seria A da Coppa Italia hudu a jere.
Ya ce ranar Asabar ne zai buga wa Juventus wasan karshe.
Tsohon golan Arsenal Wojciech Szczesny, ake sa ran zai gaji Buffon a Juventus a kaka mai zuwa.

No comments:

Post a Comment