Saturday, 19 May 2018

Gwamna da mataimakinshi sun fada ruwa garin daukar hoton Selfie a kasar Kenya

Gwamnan jihar Machakos County dake kasar Kenya tare da 'yan jaridu da suka mai rakiya da kauyawan da suka zo dan shaida bude wata sabuwar gada da ya gina a kauyen Ogembo sun fada cikin yayin da suka hau kan gadar da niyyar budeta.Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Alfred Mutua da mataimakinshi  Kisi da sauran jami'an da suka mai rakiya da 'yan jaridu suna kan sabuwar gadar ne hadda wasu daga cikin kauyawan, yayin da gwamnan ke daukar hoton dauki da kanka wanda akewa lakabi da Selfie a turance sai gadar ta rufta da su gaba daya, sukayi tsamo-tsamo cikin ruwa.

An tsamo gwamnan da mataimakinshi da sauran jama'ar inda aka garzaya dasu asibitin dake kusa, bayan an dubasu gwamnan ya bayyana cewa shi da mataimakinshi basu ji rauni ba kuma ya karyata labarin cewa lokacin yana daukar hoton dauki da kankane abin ya faru.

Saidai ya bayyana fadawa ruwan da yayi da cewa wankan babtisma ne ruwan garin ya mishi, dan haka ma zai zo garin ya gina gida.
Punch.

No comments:

Post a Comment