Friday, 18 May 2018

Gwamnoni sun kada kuri'ar yanke kauna akan shugaban 'yansanda: Su da 'yan majalisun tarayya sunce shugaba Buhari ya cireshi dan kada ya kawo mai matsala a zabe me zuwa

Tun bayan da wani bidiyo ya bayyana inda aka nuna shugaban 'yan sandan kasarnan, Ibrahim Idris lokacin daya ziyarci jihar Kano inda ake kaddamar da wani shirin leken asiri na hukumar, aka nunashi yana jawabi amma ya kama in'ina wajan fadar wata kalma akai-akai, wanda sai da ya dauki tsawon lokaci yana maimaitawa sannan ya iya fadin ta daidai, gwamnoni da 'yan majalisar tarayya sun bukaci shugaba Buhari da ya saukeshi daga wannan mukami idan kuwa ba haka ba, lallai za'a iya samun matsala a zaben shekarar 2019.


The Eagle ta ruwaito cewa daya daga cikin gwamnonin ya bayyana mata cewa, gwamnonin jihohin Rivers, Nyesom Wike da na Ekiti, Ayodele Fayose dana na APC, ciki hadda masu goyon bayan nade-naden siyasar da shugaba Buhari yayi a baya, irin su gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai duk sun kada kuri'ar yanke kauna akan shugaban 'yansandan, inda suka bukaci a koreshi kamin zaben 2019, idan kuwa ba haka ba to lallai zai iya jawa shugaba Buhari ya samu sakamakon da ba'aso a zaben.

Majiyar ta karada da cewa ba'a yiwa wannan bidiyo kwaskwarima ba, wasu da suka halarci gurin taron sun tabbatat da cewa haka abin ya faru.

Abinda ya kara tunzura wasu gwamnonin akan kiran a cire shugaban 'yansandan shine yanda baiyi abinda ya kamata ba wajan magance rikice-rikicen dake faruwa a jihohinsu ba, da irin yanda shugaban 'yansandan ya samu matsala da gwamnan jihar Benue akan rikicin makiyaya da manoma da kuma matsalar da suka samu da gwamnan jihar Nasarawa duk dai sun sa gwamnonin sun buka ci cewa cireshi daga mukamin kawai shine mafita. Ta bangaren jihar Kwara ma, Gwamna Abdulfatah Ahmad baya jin dadin yanda shugaban 'yansandan ke gudanar da al-amuran tsaron jihar, lura da yanda kwanannan ya mayar da binciken wasu 'yan kungiyar asiri da aka kama da kisan mutane wanda sukace wasu 'yan siyasane suke daukar nauyinsu zuwa Abuja, majiyar ta The Eagle ta ce yanzu fa babu gwamnan dake goyon bayan Idris.

Haka ma hatta a cikin 'yansandan yanzu Idris ya samu wandanke so a saukeshi daga mukaminshi, misali jihar Kwarar dai sunyi korafin cewa tun bayan da aka mayar da binciken 'yan kungiyar asirin da aka kama zuwa Abuja, yanzu duk wani lamari da ya taso sai ace sai an kai Abuja shugaban 'yansandan ya saka hannu sannan a dawo dashi zuwa jihar a cigaba da kes, ko kumama a mayar da kes din gaba daya Abuja, wannan yasa shuwagabannin 'yan sandan na jihohi basa iya gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali, dan sai ka fara aiki akan kes sai kaji kira daga Abuja, irin yanda aka mayar da komai sama abin akwai takaici, inji majiyar ta The Eagle.

Ta bangare 'yan majalisa kuwa tun a zaman da shugaba Buhari yayi da shuwagabannin 'yan majalisar makon da ya gabata suka shaidamai cewa su fa kawai ya cire shugaban 'yansandan daga mukaminshi, biyo bayan kiran da majalisar tamai amma yaki amsawa.

Wani dan majalisar da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC ya shaidawa The Eagle cewa duk yadda zau yi fa sai sunyi dan ganin an sauke Idris daga mukaminshi, biyo bayan abinda ya faru da Sanata Dino Melaye kuma aka kira shugaban 'yansandan yazo yawa majalisa bayani amma yaki. Ya kara da cewa wannan abin nashi zai iya shafar zaben da za'ayi a shekarar 2019 dan haka dole ya tafi kawai.

Ya kara da cewa bama idris kadai bane za'a sauke hadda me magana da yawunshi, Jimoh moshood, duk da cewa yana bin umarnin da aka bashine amma irin zakalkalewar da yake idan yana magana da tsagerancinshi yayi yawa dan haka duk tare za'a saukesu, ya kara da cewa shi yana ma mamakin yanda akayi Idris har ya samu wannan mukami.

No comments:

Post a Comment