Friday, 18 May 2018

Hadiza Gabon ta tallafawa mabukata da kayana abinci

Kamar yadda ta saba agazawa marasa galihu don ganin ta sanya su walwala, a wannan watan azumin ma jarumar finafinan Hausa, Hadiza Aliyu Gabon ta tallafawa mabukata da kayan masarufi domin gudanar da azumi cikin walwala.An nuno wadanda suka amfana da kayan abincin cikin annushuwa suna kwasar kayan masarufin tare da fatan alkairi ga jarumar.

Hadiza ko kuma Dijatou Aliyu wadda aka fi sani da Hadiza Gabon, tana daya daga cikin jarumai mata da suka shahara a farfajiyar finafinan Hausa.

Gabon ta yi matukar kwarewa a duk wani matsayi da za a ba ta a fim, wanda hakan ya sa har yau ake damawa da ita a masana'antar fim, domin ba kowace jaruma bace zata iya hawa irin matsayin da jarumar ke hawa ba a finafinai.Kyakkyawar jarumar ta kuma kasance mai yawan masoya daga cikin jaruman fim, har ta kai ga ta samu daukakar da ita kanta bata taba zaton samu ba.

Saidai ba wai daukakar da Allah ya yi wa jarumar ko kuma kwarewa da ta yi a harkar fim bane ya ja hankali na ga yin wannan rubutu ba, a'a sai don wasu kyawawan dabi'un da Allah ya azurta jarumar da su.Bayan Allah ya yi wa Hadiza baiwar kyau, ya kuma azurtata da wasu kyawawan halaye wadanda da yawan al'umma ba su da su, ba ma kawai abokan sana'arta na fim ba. Domin Hadiza ta kasance mai tausayi da jinkan al'umma domin abin hannunta bai dameta ba.

Ba na mancewa a lokacin da labarin wata yarinya mai suna "Rahma Haruna" wadda ake yawo da ita a cikin roba ana bara da ita a cikin birnin Kano ya shiga kunne Hadiza, cikin tausayi ta yi tattaki har gidansu yarinyar dake Lahdin Makole dake wajen Kano, inda ta tallafawa yarinyar da zunzurutun kudi har naira dubu hamsin #50,000 da kuma kayan abinci.Baya ga haka Hadiza ta yi matukar tausayawa yarinyar saboda irin halin da take ciki.

Bayan nan kuma Hadiza ta kan kai ziyara sansanin 'yan gudun hijirar dake sassan kasar nan, inda take agaza musu da kayan abinci da sauran kayayyakin more rayuwa. Nan ma a matsayin Hadiza na fitacciyar jaruma ta saki jikinta ga 'yan gudun hijirar domin faranta musu rai, inda tayi ta daukar hotuna dasu a matsayinta na wacce suke kallonta a finafinan Hausa kafin su shiga mawuyacin halin da suke ciki.

Bayan nan kuma a lokacin da jaruma Hadiza za ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta a shekarar da ta gabata, maimakon ta tara jama'ar da ba su dace ba ayita sharholiya, sai ta tattara kayayyakin bikin nata taje gidan marayu, inda ta dauke su a matsayin wadanda zasu taya ta bikin.

Hadiza ta yanka kek din bikin ranar haihuwartata tare da marayun.
Rariya.

No comments:

Post a Comment