Thursday, 17 May 2018

Hukumar 'yansanda da fadar shugaban kasa sunce kwaskwarima akawa bidiyon da ya nuna Shugaban 'yansanda na in'ina

Bayan da wani bidiyo ya bayyana wanda ya nuna shugaban 'yansandan kasarnan a gurin wani taro a Kano da ya halarta yana ta in'ina wajan karanta jawabinshi, me baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin kasashen waje, Abike Dabiri-erewa ta bayyana cewa sau daya ne shugaban 'yan sandan yayi kuskuren fadar kalmar amma akayi amfani da kwamfuta wajan maimaitashi.


Ta kara da cewa tana mamakin yanda wasu mutane suka yarda da abinda aka nuna a bidiyon.

Itama hukumar 'yansandan ta dandalinta na shafin Twitter tace wannan bidiyo shiryashi akayi akamai kwaskwarima, a lokacin da suke amsa wani daya tambayi abinda zasu ce akan wannan bidiyo.

No comments:

Post a Comment