Thursday, 17 May 2018

Isa A Isa shi ne gwarzon jaruman Kannywood

Jarumin fina-finan Kannywood, Isa A Isa, shi ne aka zaba gwarzon jarumai na bana a bikin karrama mawaka da 'yan wasan kwaikwaiyon arewa na Arewa Music and Movie Award AMA.


Malam Isa, wanda ya fito a fim din "Uwata ce" ya shaida wa BBC cewa karramawar ta zo ma shi da ba zata.

"Toh a gaskiya na tsinci kaina cikin wani farin ciki da ban ta ba zata zan samu a rayuwa ta ba saboda lokacin da na je wurin ance na fito a cikin jerin mutane bakwai da suka tsaya takarar kuma ban taba kawo wa ni zan samu ba", in ji shi.

Cikin jaruman da suka tsaya takarar sun hada da Ali Nuhu da Sadik Sani Sadik da Rukadawa da Ado Ahmed Gidan Dabino.

 Fim din "Uwata ce" labari ne da ke son ya isar da sako kan manyan mata masu budurwar zuciya, kuma wadanda suka shirya shi sun ce a lokacin karamar salla ce za a saki fim din.
An dai yi bikin ne a karshen makon daya wuce.

Lambar yabo ta gwarzon jarumai na cikin manyan lambobin da ake alfahari da su a duniyar fim ba wai kawai a Kannywood ba.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment