Monday, 21 May 2018

Kalli yanda wasu ma'aurata ke murnar samun 'yan Shida bayan shafe shekaru 17 suna neman haihuwa

Wadannan ma'auratannan ne 'yan Najeriya, Adebola da matarshi Ajiboye da suka shafe shekaru 17 basu samu haihuwaba, sai gashi Allah ya albarkacesu da samun 'ya'ya shida a lokaci daya, uku maza uku mata.A shekarar da ta gabatane a cikin irin wannan watan na Mayu da muke ciki, matar ta haihu a kasar Amurka ta hanyar aikin da likitoci suka mata. Shekara daya bayannan, iyayen wadannan yara sun kara fitowa dan nuna farin cikinsu da wannan arziki da suka samu.

Muna fatan Allah ya raya wadannan yara rayuwar Albarka.


No comments:

Post a Comment