Wednesday, 16 May 2018

Karanta amsar da mijin Fatima Ganduje ya baiwa wata mata da ta ce mai yayi asarar kudin sadaki

Wata baiwar Allah me saka labarai a dandalin sada zumunta na Instagram ta gayawa mijin diyar gwamna jihar Kano, Fatima Ganduje cewa Anyi asaran kudin sadaki, saboda irin kayan da fatimar ta saka, inda ta kara da cewa saura taji wani yace mata wai rayuwartace a kyaleta shashashan banza munafukan addini.Ta kara da cewa, inji wani ya ce a cikin gidane ta saka wadannan kayan saboda ta saka su a cikin motama.

Idris Ajimobi, ya kasa hadiye wannan magana da aka gayawa matarshi inda ya mayarwa da wadda tayi wannan magana da martanin, cikin harshen yarbanci da cewa, Sadakin kakarkine akayi asara, (kamar yanda yarbawan suka fassara).

Matar ta sake mayarwa da Idris amsar cewa, bansan abinda ka rubuta da yarbanci ba amma na dan iya gane kadan, kaje kasan mutuncin mutane farko, sannan kuma ka koyi kishin matarka, saboda irin shigar da take yi, addinin musulunci ko na kiristanci babu wanda yace mace ta rika shiga tsirara-tsirara.

Takara da cewa kaje ka koyi addinin da kake ikirarin kana yi, maimakon ka mata gayara akan irin abinda take yi kazo kana kareta, ba laifinka bane, laifin irin tunanin da yasa ka auretane wai kana tunanin ka auri bafulatanan da tafi kowacene, sai an jima, kuji dadinku.

Idris ya sake bata amsar cewa yana mutunta wanda yasan mutuncin kanshine kawai.

No comments:

Post a Comment