Monday, 14 May 2018

Karanta labari me ban tausai: Miji ya rasu wajan tseratar da matarshi da wutar lantarki ta kama

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN a takaice ya ruwaito daga jihar Bauchi cewa wani bawan Allah me suna, Salihu Yahaya ya rasa ranshi lokacin da yaje ceton matarshi da ta makale a jikin wutar lantarki, yanda lamarin ya faru kuwa shine.

Matar marigayin ta shimfida tabarma me lema ne a kan wayar wutar lantarkin da ta huje da niyyar yin shanya, aikuwa tana shimfida tabarmar sai wutar ta rike ta nan ta nemi dauki, a lokacin mijinta na yin alwala dan zuwa sallar la'asar.

Da yaga yanayin da ta shiga, sai ya taso, hannunshi da lemar alwala ya kama wayar da hannunshi dan ya tseratar da matar tashi, yayi nasarar janye wayar kuma matar tashi ta kubuta, nan kuwa wutar ta rangadashi da kasa, haka aka kwashehi zuwa Asibiti, amma kamin a karasa sai yace ga garinku nan, kamar yanda wani yaronshi, Sani Ahmad ya bayyana.

Ita dai matar ta kubuta, an kaita asibiti an bata magani yanzu ta dawo gida ta fara samun sauki.

Muna fatan Allah ya jikanshi.

1 comment: