Monday, 14 May 2018

Levante ta karyawa Barcelona kadari

Yunkurin Barcelona na kafa tarihin kammala wasanni a gasar La liga ba tare an doke ta ba ya gamu da cikas.


Kungiyar Levante ce dai ta doke Barcelona da ci 5-4 a wasan da suka buga ranar Lahadi.

Tun da farko dai Levante ta lallasa ta ne da ci 5-1 inda Emmanuel Boateng ya zura kwallaye uku yayin da Enis Bardhi ya zura kwallaye biyu.

Sai dai dan wasan Barcalona Philippe Coutinho ya zura kwallaye uku inda kuma Luis Suarez ya ci kwallo daya a bugun fenareti.

Barcelona dai ta buga wasanni 44 a gasar La Liga ba tare da an doke ta ba inda ta shafe tarihin da Real Sociedad ta kafa na buga wasanni 38 ba tare da an doke ta ba a kakar wasa ta 1979/80.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment