Sunday, 20 May 2018

Likitoci a Yola sun raba jariran da aka haifa a hade

Likitoci a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Yola jihar Adamawa sunyi nasarar raba wasu jarirai 'yan watanni hudu da aka haifa cikinsu a hade, aikin da ya faru bisa jagorancin babban likitan asibitin Farfesa Auwal Abubakar ya bayyana cewa shine irinshi na biyu da suka taba yi.


A wani taron manema labarai da aka gudanar Farfesa Auwal ya bayyana cewa ranar 14 ga watan Mayu suka gudanar da wannan aiki kuma aikin ya daukesu awanni hudune kamin su kammalashi, haka kuma jariran zasu iya rayuwa ba tare da wata matsalaba bayan da aka rabasu.
Ya kara da cewa Najeriya nada kwararrun ma'aikatan Lafiya da zasu iya yin gogayya dana kowace kasa.
Mahaifin yaran, me suna Muhammad Ramat daya fito daga Kasuwar Shanu, Maiduguri ya godewa hukumar gudanarwar Asibitin da ta biya kudin aikin da akawa 'ya'yanshi.

No comments:

Post a Comment