Tuesday, 22 May 2018

'Ma'aikata, Musulmai ku dauki hutun aiki: Yin Azumi na da hadari ga Al'umarmu>>inji wata ministar kasar Denmark


Wannan wata minista ce a kasar Denmark me suna Inger Stojberg dake da matsanancin kin jinin baki, ta fito jiya Litinin tace musulmai su daina fitowa aiki saboda Azumin watan ramadana da sukeyi, dalilinta kuwa shine wai yin Azumin yana da hadari ga jama'ar kasar.


Ministar tayi bayani kamar haka:

Ina son yin kira ga musulmi da su dauki hutun aiki saboda Azumin watan Ramadana da sukeyi dan gujewa faruwar wani mummunan abu ga jama'ar kasar Denmark da hakan ka iya jawowa.

Bana tunanin addinin daya bayar da umarnin yin aiki da hukunce-hukunce tun shekaru dubu daya da dari hudu zai iya dacewa da zamantakewarmu da kuma yanayin ayyukanmu a kasar Denmark.

Tace yin azumi zai iya shafar aikin da akeyi da kuma lafiyar jama'a inda ta bayar da misali da direban mota wanda be ci abinci ba ko kuma yasha wani abuba har na tsawon awanni 10.

Ta kara da cewa wannan abune me hadari ga dukkan mu.
The local dk.

No comments:

Post a Comment