Monday, 14 May 2018

Majalisar Limamai Da Malamai Ta Jihar Kaduna Ta Yi Allah Wadai Da Tsine-tsinen El Rufa'i

Da yake jawabi a yayin wani taron manema labarai da Majalisar ta kira a Ofishin ta dake Garin Kaduna, Shugaban Majalisar Malaman Sheikh Usman Abubakar Baban Tune, yace ya zama wajibi a garesu a matsayin su na Malaman Addinin Musulunci da su fito su shelantawa Duniya takaicin su gami da yin Allah wadai da kalaman Gwamnan. 


Sheikh Baban Tune ya cigaba da cewar, ko kadan bai dace ba ace ana samun muggan kalamai da tsine tsine daga bakin Shugaba ba, domin Shugaba nagari ba'a san shi da haka ba, saboda Shugaba nagari yana umarni da zaman lafiya da kaucewa faruwar fitina ne, amma ba wai a samu Shugaba da hannu dumu dumu wajen yada fitina da umarnin tayar da zaune tsaye, ta hanyar umartar aci zarafi ko a wulakanta wasu saboda wani bambanci na siyasa ba. 

Malaman sun kara da cewar, ita kalmar tsinuwa bata faduwa kasa a banza, idan wani ya bude baki ya tsinema wani ko wasu, to tsinuwar nan zata tashi sama ne tayi gabas tayi yamma sannan tayi kudu da Arewa, idan bata samu muhallin zama ba sai ta dawo kan wanda aka tsinemawa, idan ya tabbata bai da alhakin wannan tsinuwa, to sai tsinuwar ta dawo kan wanda ya furtata na asali tayi munmunan aiki a kanshi, ashe kuwa tsinema wani ko da Dabba ne yana da hatsari matuka ballantana tsinewa Dan Adam, kuma abin bakin ciki tsinuwar ta fito ne daga bakin wanda yake a matsayin Shugaba. 

Majalisar Limamai da Malaman sun koma koka gami da yin tir da matakan da Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka ta hanyar yi wa Jama'ar Jihar karfa karfa a yayin zaben kananan hukumomin da ya gabata, inda aka tauye hakkin 'yan takara da dama akayi dauki dora kawai, bisa ga wannan a matsayinsu na shugabannin addini ba za su rungume hannu su zura ido ana irin wannan saka da mugun zare ba, dole ne su fito fili su fadi gaskiya, kuma matukar Gwamnan bai dawo hayyacin shi ba, za suyi amfani da damar dake hannun su a Mambarorin masallatan Juma'a da wuraren wa'azi domin ankarar da jama'a hatsarin zabar Shugabanni masu irin wadannan halaye. 

Sai dai a mayar da martani da yayi akan Majalisar Limaman, Shugaban hukumar kula da harkokin addinai ta Jihar Kaduna Injiniya Muhammad Namadi Musa, ya nuna damuwar shi dangane da rashin bin koyarwar addini da Malaman su kayi ta kasa bin hanyar da ya kamata wajen yin nasiha ga mai girma Gwamnan, inda suka dauki matakin yin yekuwa ta kafafen yada labarai, amma duk da haka ya kamata Malaman su sani cewar Gwamna Mutum ne ajizi zai iya yin kuskure, kuma idan yayi kuskure akwai yadda addini ya tanada ayi mishi nasiha a addinance ba'a siyance ba, kuma dangane da korafin cewa anyi karfa karfa a zaben kananan hukumomi da akayi a jihar, ya kamata Malaman da sauran jama'a su fahimci adalci na Gwamna El Rufa'I domin a kananan hukumomi 23 da ake da su a Jihar, Jam'iyyar adawa ta PDP ta lashe zabe a wasu kananan hukumomin jihar, sabanin yadda yake faruwa a wasu Jihohin inda ake haramtawa Jam'iyyun adawa koda kujerar Kansila.
rariya.

No comments:

Post a Comment