Thursday, 17 May 2018

Messi da Suarez sun kawo ziyara Afirka

Kungiyar Barcelona ce ta lashe gasar Laliga a bana
'Yan wasan kungiyar Barcelona sun isa kasar Afirka ta Kudu inda za su buga wasan sada zumunci da kungiyar Mamelodi Sundowns ranar Laraba.


Jami'an tsaro sun raka 'yan wasan cikin filin jirgin saman da suka sauka a lokacin da suka isa Afirka ta Kudu
Tawagar ta 'yan wasan dai ta samu rakiyayar jami'an tsaro a lokacin da suka isa filin jiragen sama na OR Tambo da ke birnin Johanesburg.
Masu sha'awar kwallon kafa sun yi daukar 'yan wasan da wayoyinsu na salula a lokacin da suka sauka a filin jirgin sama na OR Tambo dake birnin Johanesburg
Kuma jerin mutane sun taru a filin jirgin saman domin ganin shahararrun 'yan wasan, kuma sun yi ta daukar hotunan 'yan wasan.
Tuni dai 'yan wasan suka fara hutawa a kasar ta Afirka ta Kudu
bbchausa.

No comments:

Post a Comment