Saturday, 19 May 2018

Mikel Arteta ya amince ya zama sabon kocin Arsenal

Tsohon dan wasan Arsenal Mikel Arteta ya amince ya zaman sabon kocin kungiyar wanda zai maye Arsene Wenger, duk dadai cewa babu wata takarda da ya sakawa hannu a wannan yarjejeniya amma ana saran nan bada dadewaba hakan zata faru.Yanzu dai haka Arteta shine mataimakin kocin kugiyar Manchester City, Pep Guardiola kuma ya taka muhimmiyar rawa wajan taimakawa kugiyar samun nasarar da tayi a kakarwasan bana.

Shugaban kungiyar Arsenal Ivan Gazidi ya zabi Arteta ne saboda yana tunanin cewa matashin koci zaifi kawo abinda ake tsammani a Duniyar wasa a yanzu.

Arteta ya bar Arsenal bayan da yayi ritaya daga buga wasa a shekarar 2016, inda ya buga mata wasanni dari da hamsin kuma yaci kwallaye goma sha shida da kuma bayar da taimakon cin kwallaye goma sha daya, kamar yanda Goal.com ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment