Monday, 14 May 2018

Muhammad Salah ya lashe kyautar takalmin zinare

Tauraron dan kwallon kafa, Muhammad Salah ya lashe kyautar takalmin zinare bayan da ya zama wanda yafi cin kewallaye da yawa a gasar Firimiya ta kasar Ingila a bana, Salah na da kwallaye talatin da biyu wanda hakan yasa ya wuce Harry Kane dan Tottenham.


Salah dai shine na biyu a nahiyar Afrika, bayan Drogba da ya taba lashe wannan kyauta.

A lokacin da yake hira da manema labarai, Salah ya bayyana cewa zai sake yin iya kokarinshi dan yaga cewa ya lashe irin wannan kyautar a shekara me zuwa.No comments:

Post a Comment