Thursday, 17 May 2018

Muhimmancin binciken wadanda suka kashe mutane a jihar Kwara yasa aka mayar da kes din Abuja: Hukumar 'yansadna ta musanta cewa shugabanta na kokarin gogawa Saraki kashin kaji

Hukumar 'yansandan kasarnan ta karyata batun da kakakin majalisar dattijai Bukola Saraki ya fitar na cewa shugaban 'yan sandan, Ibrahim idris na yunkurin gogamai kashin kaji ta hanyar hadashi da laifi irin wanda akawa sanata Dino Melaye.


Shi dai Bukola Saraki ya zargi cewa shugaban hukumar 'yan sandan na shirin bata mai suna da gwamnan jihar Kwara, bayan da aka mayar da binciken wasu 'yan kungiyar asiri da ake zargi da kashe mutane goma sha daga Abuja daga jihar ta Kwara.

Saidai a nata martanin hukumar 'yansandan ta bayyana cewa wannan zargi da Bukola Saraki yayi bashi da tushe ballantana makama, domin har yanzu ana cikin binciken masu laifinne tukuna.

Ta kara da cewa, mutanen da aka kama sun amsa laifin cewa sun kashe mutane goma sha daya a cikin jihar ta Kwara dama wasu jihohin Najeriya kuma wasu manyan mutanene suka dauki nauyinsu, saboda muhimmancin wannan kes nasu shiyasa aka bukaci a mayar dashi Abuja dan gudanar da sahihin bincike kamin a gurfanar dasu gaban kotu.

Hukumar 'yansandan ta kara da cewa yin magana akan wani kes da ake cikin bincike akanshi laifine, kuma duk wanda aka kama yana da hannu akan wannan kes to komi matsayinshi ba za'a daga mai kafa ba, ta kuma kara da cewa ba kes din masu laifin jihar Kwara kadaine aka mayar Abuja ba, akwai na wasu sauran jihohi da aka mayar saboda muhimmancinshi, dan haka 'yan Najeriya su yi watsi da waccan magana ta Bukola Saraki.

No comments:

Post a Comment