Thursday, 17 May 2018

Rikicin Benue: A shirye nike in ajiye mukamina>>Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa a shirye yake ya bar kujerar mulkinshi domin be dauke ta wata tsiyaba, yayi wannan batunne a jihar Benue a matsayin martani da yake mayarwa ga wani fasto da ya zargeshi da cewa yayi shiru ya kasa magana yayin da ake ta kashe kiristoci Saboda shi mataimakin shugaban kasane.Osinbajo ya bayyana cewa be roki a bashi mukamin da yake kai na mataimakin shugaban kasa ba, dan haka ba wani abubane a gurinshi, zai iya barinshi cikin dan kankanin lokaci idan hakan ta taso, ya kara da cewa lamuranshi na hannun Allah ba wani mutum ba.

Ya kuma ce shi ba dan siyasa bane, kamar yanda faston yace shima ba dan siyasa bane, shi kiristane wanda yanzu ya shiryu, kuma bazai taba barin addininshi a kasa ba saboda wani abu da zai samu, ya kara da cewa a lokacin da annabi Isa ya bayyana a gareshi ya bayyana mishi cewa a kwai wani sashi na Imani da ba'a iya ganinshi, saboda da haka yayi amannar cewa dalilin wannan bangare na Imani da ba'a ganine yasa ya zama mataimakin shugaban kasa.

Haka kuma Osinbajo ya musanta maganar wani mutum shima da yake cewa gwamnatin tarayya na da shirin musuluntar da Najeriya da kuma kawar da wata karamar kabila daga doron kasa saboda bata da wani me fada aji da zai tsaya mata. Yace babu wani mutum me hankali da zai kashe mutanenshi.

Osinbajo ya bayyana cewa babu abinda zasu iyayi ga wadanda suka rasa rayukansu, saidai zasu yi kokarin inganta rayuwar wadanda suke raye a yanzu dan su yi rayuwa me kyau, ya kara da cewa shugaban kasa M. Buharine ya aikashi jihar dan tabbatarwa da al-umma cewa zasu tallafawa musamman masu gudun hijira da rikicin fulani da manoma ya shafa da kuma sauran ayyukan more rayuwa a jihar.

Gwamna Ortom ya yabawa Gwamnatin tarayya akan irin jami'an tsaron data saka a jihar dan kawo karshen wannan riki.
Vanguard.

No comments:

Post a Comment