Wednesday, 23 May 2018

'Saida aka tsayar da kowa Pobga yayi dawafi'>>Nazir Ahmad

Kamar yanda mukaji labari, tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad yaje aikin Umrah. Nazir ya bayar da labarin zuwa dan wasan Manchester United, Paul Labile Pogba Ka'aba, inda yace saida aka tsayar da kowa Pogban ya gama dawafi.


Nazir yace, dan wasan Manchesternnan dai, Pogba da aka sani, saida suka gama wahala, suka gama tirmutsutsu, sai ga shinan da jami'an tsaro, aka tsayar da kowa yaje ya shiga inda suka yi ta wahalar shiga cikin sauki yayi Dawafi, yace, wani malain ma be iya yaje ba.

Nazir yace amma lokacin suna yara haka malamai zasu yi ta bayar da fatawa suna zagin  kwallo, to wallahi kamar yanda Pogba yazo da jami'an tsaronnan haka ranar Qiyama, wanda baka tsammani zaka ga gashi can ya shige Aljanna amma kai kana nan baka shigaba.

Saurari bidiyonnan na kasa dan jin cikakken abinda Nazor ya fada:

No comments:

Post a Comment