Friday, 18 May 2018

Sakataren harkokin wajen Amurka ya kira shugaba Buhari: Amurkar ta yabawa Najeriya

Sakataren harkokin kasashen wajen kasar Amurka, Mike Pompeo ya kira shugaban  kasa, Muhammadu Buhari inda ya tabbatar da dadaddiyar dangantakar dake tsakanin kasar Amurkar da Najeriya.


Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta kasar ta fitar da sanarwar cewa, jiya Alhamis Mista pompeo ya kira shugaba Buhari  inda ya jaddada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu  ya kuma tabo batun ziyarar da shugaba Buharin yakai kasar ta Amurka, watan da ya gabata.

Yace suna jindadin yanda Najeriya ke jagorantar kasashen Afrika musamman akan abubuwan da suka yi tarayya akai da suka hada da: Tsaro, yaki da ta'addanci da rashawa da cin hanci, samar da hanyoyin habaka tattalin arziki da kuma tabbatar da mulkin Dimokradiyya.

Ya kuma ce zasu ji dadin cigaba da wannan dangantaka da Najeriya wajan cigaban kasashen biyu.


No comments:

Post a Comment