Wednesday, 16 May 2018

Sarkin Musulmi Ya Tabbatar Da Ganin Watan Ramadan

Mai Alfarma Sarkim Musulmi Sa'ad Abukar lll, ya bayyana ganin watan Ramadan a yau, a wurare daban daban da suka hada da Sokoto, Maiduguri, Damaturu, Dutse, Potakot da sauransu. 


Ya bayyana gobe Alhamis ya zama daya ga watan Ramadan, don haka za a tashi da azumi goben. 

Yayi kira ga al'umma da a dage da ibada a cikin wannan watan don dacewa da rahamar dake ciki. 
rariya.

Shafin Hutudole.com na yi wa al'ummar Musulmi barka da shigowar Watan Ramadan 1439.

No comments:

Post a Comment