Tuesday, 22 May 2018

Saura kadan dana sayi Ronaldo: Rashin kudi yasa Man U suka min shigar sauri

Tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger a lokacin da yake ficewa daga kungiyar, bayan ya ajiye aiki ya bayyana cewa kadan ya rage da shi zai sayi tauraron dan kwallonnan, Cristiano Ronaldo amma rashin kudi yasa Manchester United suka mai shigar sauri suka saye Ronaldon.


Wenger dai yayi suna wajan bayyana cewa sauran kadan ya sayi taurarin 'yan wasa, taurarin 'yan kwallon da ya taba fadar cewa saura kadan ya sayesu sun hada da, Zlatan Ibrahimovic, Ngolo Kante, Vincent Kompany da Lionel Messi.

Wannan karin kuma kan Ronaldo abin ya fado. Shi dai Ronaldo ya fara wasanshi lokacin yana matashi a Sporting Lisbon amma yazo Man U tauraruwarshi ta haskaka daga nan kuma ya wuce Real Madrid inda yaci gaba da samun daukaka.

Wenger yace a shekarar 2003 Ronaldo da mahaifiyarshi sunzo kuma sun fara magana akan sayan nashi akan kudi Yuro miliyan hudu, saura kadan a kammala zancen.

Man U sunyi wasa da Lisbon suka ga yanda Ronaldo ke wasa, kawai sai labari Wengern yaji cewa Man U din sun sayi Ronaldo akan Yuro miliyan sha biyu, ya kara da cewa a wancan lokacin ba zasu iya sayanshi akan wancan kudin ba saboda basu da kudi.

Wenger ya kara da cewa lokuta da dama zaka rika tunanin dama abu kaza kayi amma idan ana ciniki dolene mutum ya san irin farashin da zai amince dashi.

Ya kara da cewa kai ya kake tunanin zata kasance da ace na hada Thierry Henry da Cristiano Ronaldo a guri guda suna wasa. Tabbas da irin nasarar da zan samu a Arsenal ba 'yar kadan bace.

No comments:

Post a Comment