Thursday, 17 May 2018

Shugaba Buhari ya aikewa musumai da sakon taya murnar shiga Azumi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya aike da sakon taya murnar shiga watan Azumin Ramadana ga musulmai inda yayi kira a garesu da su yi amfani da wannan lokaci dan taimakawa gajiyayyu da kuma taimakawa gwamnati cimma muradunta.


A sanarwar da me magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari yayi kira ga musulmai da suyi koyi da halayen fiyayyen halitta, Annabi Muhmmad (S. A. W) wajan nuna tausai da taimakawa gajiyayyu inda yace azumi ba yunwa da kishirwa bane kawai, hanyace ta tsarkake kai da gyara ayyuka.

A karshe yayi addu'ar Allah ya baiwa musulmai ikon kammala wannan Azumi lafiya.

No comments:

Post a Comment